Connect with us

Featured

Ƴanbindiga Sun Yi Ajalin Wasu Mutane a Kwara

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da wani ya jikkata, a wani harin da ake zargin ‘yan bindiga suka kai garin Eruku da ke kan iyakar Ekiti LGA da jihar. A cewar rundunar, maharan sun afkawa cocin Christ Apostolic Church yayin gudanar da ibada, inda suka kashe mutum ɗaya a ciki, sannan daga bisani aka gano gawar wani a cikin daji bayan maharan sun tsere.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga cocin ne da yammacin Lahadi yayin wani taron musamman, inda suka bude wuta suka kashe mutane uku nan take, sannan suka yi garkuwa da limamin cocin da wasu mambobin. Daga bisani kuma sun tare matafiya a kan titin Ilorin–Kabba, lamarin da ya tilasta mutane tserewa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Wasu mazauna garin, ciki har da shugabannin al’umma, sun bayyana tsantsar tsoron da suke ciki, suna cewa wannan hari na baya-bayan nan na cikin jerin hare-haren da suka addabi Eruku cikin makonni uku. Sun roki gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa, suna mai cewa an bar su cikin hali na fargaba da rashin tsaro.

Rundunar ‘yan sanda ta ce jami’anta tare da vigilante sun yi gaggawar kai dauki, amma maharan sun tsere cikin daji. Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yaba da jajircewar jami’an tsaro, tare da tabbatar wa da jama’a cewa za a ci gaba da kai farmaki kan miyagun har sai an kawar da su gaba ɗaya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahisholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet