Connect with us

Featured

Kwankwaso Zai Samu Kuri’u Miliyan 10 a Kano a 2027 — NNPP

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashim Suleiman Dungurawa, ya bayyana cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na sa ran samun akalla kuri’u miliyan 10 daga Kano kawai a zaben shugaban ƙasa na 2027. Dungurawa ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi shugabannin Kano Online Media Chapel na NUJ a ofishinsa, inda ya ce matsalolin da jam’iyyar ta fuskanta a 2023 ya samo asali ne daga rashin rubuta tambarin jam’iyyar a fili a takardar kuri’a wanda ya rikita masu kada kuri’a da dama.

A cewar Dungurawa, matuƙar aka zaɓi jagoran na NNPP a 2027, to zai maida hankali ne kan aiwatar da irin nasarorin da ya samu lokacin da yake gwamna a Kano a shekara ta 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015. Ya ce daya daga cikin manufofinsa shi ne tura yara 1,000 ’yan talakawa daga kowace jiha 36 karatu a ƙasashen waje kyauta. Haka kuma, ya bayyana shirin Kwankwaso na ɗaukar jami’an tsaro miliyan guda-guda — sojoji, ’yan sanda, DSS da Civil Defence — domin farfaɗo da tsaro da kawo karshen kashe-kashe a sassan ƙasar nan.

A cikin jawabin nasa, Dungurawa ya yabawa gwamnatin Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf kan ababen more rayuwa da ci gaban ilimi da ta samu. Ya kuma yi kira ga kungiyar Kano Online Media Chapel da su ci gaba da yada bayanai nagari domin amfanin jama’a, tare da nuna sha’awar haɗa kai da su wajen isar da manufofin NNPP ga al’umma.

Shugaban kungiyar, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya ce ziyarar ta su na da nufin gabatar da sabbin shugabannin kungiyar tare da kulla haɗin kai da jam’iyyar NNPP. Ya tabbatar wa shugaban NNPP na jihar cewa za su ci gaba da bayar da rahotanni cikin adalci, daidaito da bin ka’idar aikin jarida a duk faɗin Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet