Connect with us

Featured

Ganduje Ya Yi Allah-wadai Da Hare-haren Ƴanbindiga a Shanono Da Tsanyawa

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Shanono da Tsanyawa, inda mutane uku suka rasa rayukansu aka kuma yi garkuwa da mata da yara da dama. Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, bakin ciki da tayar da hankali,” yana mai cewa irin wannan hari barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a.

Ganduje ya jajanta wa iyalan mamata da mutanen yankunan da abin ya shafa, yana jaddada bukatar gaggawar agaji da hadin gwiwa tsakanin hukumomi da jami’an tsaro domin magance tashin hankali. Ya bukaci Gwamnatin Kano ta dauki matakan tsaro na zamani da suka hada da leken asiri, sa-ido na al’umma da karfafa rundunonin sa-kai. Ya kuma tunasar da tsarin tsaro da gwamnatinsa ta yi shekaru 2015–2023, wanda ya ce ya rage matsalar ta’addanci da laifuka a jihar.

Ganduje ya yaba wa gwamnatocin Nijar, Kwara, Kebbi da sauran jihohi bisa yadda suka fuskanci irin wadannan kalubale ba tare da bata lokaci ba. Haka kuma, ya yi maraba da kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sabunta rundunar soji da karfafa garkuwar tsaro ta kasa. Ya shawarci jama’a su kwantar da hankali amma su kasance masu sa ido tare da ba da bayanai ga hukumomin tsaro.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet