Connect with us

Featured

Bai Kamata Gwamnatin Kano Ta Siyasantar Da Batun Tsaro Ba – Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya musanta zargin da Gwamnatin Kano ta yi masa cewa ya fadi magana da ka iya kawo cikas ga kokarin tsaro. Ya bayyana cewa maimakon siyasantar da lamarin, ya dace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tashi tsaye wajen magance matsalolin da ke addabar jihar.

Sanata Barau, cikin wata sanarwa da mai taimaka masa Ismail Mudashir ya fitar, ya kalubalanci gwamnati ta fitar da bidiyon da ke nuna wai ya yi batu da zai dagula tsaro. Ya ce shi kullum yana aiki tare da hukumomi domin ganin an dakile barazanar ‘yan daba da ‘yan bindiga da ke shiga wasu yankuna na Kano. Kakaki24 ta ruwaito cewa Barau ya zargi gwamnatin Kano da ƙirƙiro karya domin ɓata sunansa.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta yi kasa a gwiwa wajen gudanar da mulki yadda ya dace, lamarin da ya janyo koma-bayan da Kano ta samu a ‘yan shekarun nan. Ya ce jihar na da duk abin da ake bukata don dawowa matsayin baya, amma babu matakin da gwamnan ke dauka. Ya kuma zayyano tallafin da ya bayar ga rundunar ‘yan sanda, DSS, da sauran hukumomin tsaro domin kara inganta tsaro.

Sanatan ya ce ya raba motocin aiki da babura ga jami’an tsaro, ya gyara sassan hedikwatar ‘yan sanda, ya gina ofisoshi, tare da kawo makarantu na horarwa ga NSCDC, PSC da Immigration a wasu kananan hukumomi. Ya ce haka da hasken tituna da ya saka a daruruwan wurare ya taimaka matuka wajen sintiri da kare al’umma a Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet