Featured
Budaddiya Wasikar Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano Kan Matsalar Tsaro

Daga Abu Fouad
Mai Girma Gwamna Yusuf,
Ina fatan wannan wasiƙa ta same ka lafiya. Na rubuta ba don raini ba, sai don fatan ta isa gare ka cikin gaggawa. Ta hanyar amfani da tsofaffin kafafen sadarwa da sababbi—masu saurin isar da saƙo—ina turo maka wannan wasiƙa a matsayina na ɗan ƙasa mai damuwa da halin ƙara ta’azzarar matsalar tsaro da ta mamaye al’ummominmu.
Ko da yake Kano ta dade tana cikin kwanciyar hankali fiye da makwabtan jihohi, yarjejeniyar “sulhu” da aka kulla a Jihar Katsina kwanan nan ta ƙara jefa Kano cikin haɗari, musamman kananan hukumomin da ke iyaka da Katsina. Yiwuwar ƙaruwa da matsalolin tsaro a jiharmu na da alaƙa da motsin ’yan fashi da suka shiga Kano.
Waɗannan miyagun mutane na ci gaba da addabar al’ummomin kan iyaka, suna tsoratar da mazauna yankuna, suna dakile harkokin yau da kullum. A kwanakin nan, tashin gwauron zabi na sace-sace da hare-haren ta’addanci kan mazauna karkara ya bar jama’a cikin fargaba, ya dakatar da al’amuran yau da kullum, ya kuma bar mu cikin wani mawuyacin hali. Mummunar tasirin lamarin ta bayyana a yadda aka bar wasu kauyuka a Tsanyawa da Shanono, inda iyalai suka tsere domin neman tsira. Wannan ba wai lissafi ba ne kawai; gaskiya ce da kowane ɗan asalin Kano ke rayuwa da ita—musamman mata, yara, da tsofaffi.
Kwantar da hankali da samar da tsaro wani haƙƙi ne na asali da gwamnati ta ɗauki alhakin bayarwa. Amma a halin yanzu, kamar gwamnati a matakai daban-daban tana kokarin kare jama’a—wannan babban nauyi da suka rantse za su yi. Miyagu sun lura da gibi ko rauni a bangaren siyasa kuma suna cin gajiyar hakan. Dole mu tuna cewa tabbatar da doka da oda aikin kowa ne; rashin tsaro ba ya bambanta tsakanin mutane, kuma illolinsa sun yi fadi. Saboda haka, ƙara tabarbarewar tsaro a Kano ta zama babban abin damuwa ga kowa.
A yau, Kano—jihata, gidana—na fuskantar babbar barazanar tsaro. Amma wasu “mutane Wanda basu San kansu ba” suna bin kafafen sada zumunta suna zagin duk wanda ya nuna damuwa, suna cin zarafinsa ta a yanar gizo. Waɗannan mutane masu son kai, masu sayar da lamirinsu kan ƙananan abubuwa, na fahimtar kowace kiraye-kirayen na gyara kayan Ka a matsayin batanci ga Gwamna ko gwamnatin sa. Sun manta cewa a lissafe tsaro ana aunawa ne da irin natsuwar da ’yan ƙasa ke ji a kowace rana.
Ina roƙon jagorancinka da ka dauki mataki cikin gaggawa—ka ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da tsarin gargajiya, wanda tarihi ya nuna shi ne garkuwar al’ummominmu—domin tabbatar da cewa makomar Kano ba ta lalace saboda tsoro. Duk da bambancin siyasa, ’yan Kano a shirye suke su goyi bayan duk wani tsari da zai kawo zaman lafiya mai dorewa.
A wannan ruhin, ina miƙa waɗannan shawarwari cikin tawali’u domin la’akari:
A ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro na jiha da shugabannin gargajiya, domin su ne mafi kusa da al’umma, kuma za su iya bayar da bayanan sirri cikin lokaci.
A tura ƙarin jami’an sintiri masu motsi zuwa yankunan da ke cikin haɗari domin samar da tsaro da takaita ayyukan ta’addanci.
A haɗa fasahohin zamani—musamman na’urar jirgi mara matuƙi (drones) masu arha—cikin ayyukan tsaro. A karkara inda manoma da al’umma suke fuskantar barazana, waɗannan drones za su taimaka wajen sintiri da gano matsaloli cikin lokaci.
A sanye drones da na’urorin hangen dare da “thermal cameras” domin bibiyar gonaki da yankunan kan iyaka, suna turo bayanai kai tsaye zuwa cibiyar ba da umarni. Za a iya horas da mazauna yankuna a matsayin “masu lura da drones,” su na aika bayanai ta hanyar manhajar waya da aka haɗa da cibiyar tsaro.
A haɗa bayanan da aka tattara cikin tsarin gaggawa na jiha don inganta aiki tare tsakanin ’Yan Sanda, Sojoji, NSCDC, da kungiyoyin sa-kai na tsaro.
A tallafa wa kungiyoyin sa-kai da horo da kayan aiki na zamani, tare da saka idanu sosai don kauce wa aikata ba daidai ba.
A gaggauta samar da muhimman ayyukan more rayuwa—hanya, sadarwa, hasken unguwanni—domin rage warewar al’umma da ƙara tsaro.
A kafa tsarin amsa gaggawa don karɓa da magance matsaloli, tare da tsare-tsaren lokacin aiwatarwa.
A fitar da umarnin zartarwa da zai ayyana kananan hukumomin da ke iyaka da Katsina a matsayin yankunan da aka ƙara tsaro (“militarized zones”) domin murkushe ’yan bindiga.
A warware duk wata rashin fahimta—idan tana akwai—tsakaninka da sauran shugabannin hukumomin tsaro a jiha, tare da aiki a hade domin tabbatar da nasara a yaki da rashin tsaro.
Da girmamawa,
Abu Fouad
Ɗan ƙasa mai damuwa daga Jihar Kano