Featured
Tinubu Ya Sanya Farfesa Yakubu Cikin Mutane 32 Da Za a Naɗa a Matsayin Jakadun Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, cikin jerin mutum 32 da zai aika wa majalisar dattawa domin neman sahalewarta. Wannan na zuwa ne kusan wata biyu bayan kammala wa’adinsa na biyu a matsayin shugaban hukumar zabe ta ƙasa.
Farfesa Mahmud ya kammala aikinsa a farkon watan Oktoba 2025, bayan jagorantar zabukan ƙasa na tsawon wa’adi biyu. Sabon naɗin nasa ya taso ne a wani lokaci da ƙasar ke kokarin cike guraben jakadun da suka dade ba a tura sabbi ba.
Masana harkokin diplomasiyya sun sha bayyana cewa rashin nadin jakadu sama da shekara biyu ya kawo koma baya ga hulɗar ƙasa da ƙasashen waje. Kakaki24 ta tattara cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin gyara wannan gibi ta hanyar tura sababbin wakilai da suka samo daga fannoni daban-daban.
Majalisar dattawa na sa ran tattauna sunayen cikin makonni masu zuwa, kafin ta yanke hukuncin amincewa ko ƙin amincewa da su. Idan aka tabbatar da nadin, Mahmud Yakubu zai shiga jerin manyan jami’an diplomasiyyar da ke wakiltar Najeriya a kasashen waje.
