Connect with us

Featured

Kashi 70% Na Mutanen Da Ke Cikin Gwamnatin Tinubu Sun Yi Adawa Da Shi a Baya — Bwala

A wani bayani da ya jawo ce-ce-ku-ce, Daniel Bwala, mai ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na mutanen da ke aiki tare da Shugaban a yau sun taba adawa da shi a baya. Ya bayyana haka ne a shirin Morning Show na Arise TV yayin da ake musayar ra’ayi kan sabbin jerin sunayen jakadu da Shugaba Tinubu ya turo wa Majalisar Dattawa domin tantancewa.

 

Bwala ya ce wasu na ganin akwai wadanda ba su cancanta ba saboda sun taba sukar Tinubu a baya, amma ya nusar da cewa siyasa cike take da rikice-rikice da sabani. Ya kara da cewa Tinubu kansa ya taba shaida masa cewa mahaifiyarsa ce ta koya masa cewa kar ya taɓa kullatar wadanda suka saba masa, domin idan ka cigaba da fushi da kowa, wata rana ba za ka sami wanda za ka jagoranta ba.

 

A cikin takaitaccen tattaunawar, Bwala ya ce tun haduwarsu ta farko a Janairu 2024, Tinubu ya nuna masa cewa baya daukar adawa a matsayin dalilin kiyayya. Ya kuma bayyana cewa kusan dukkan manyan mutanen da ake gani tare da shugaban a yau— ciki har da wadanda aka saka cikin jerin jakadu — akwai wadanda suka taba aiki a gabansa ko ma sukar sa.

 

Punch ta ruwaito cewa jerin sunayen jakadu da Shugaba Tinubu ya mikawa Majalisar sun hada da Farfesa Mahmood Yakubu, Reno Omokri, Femi Fani-Kayode, da Ifeanyi Ugwuanyi, tare da karin wasu mata guda goma a matsayin jakadu. Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya ce za a bayyana kasashen da kowane daga cikin mutanen zai tafi ne bayan tantancewa a majalisa.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet