Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Buƙaci Kotuna Su Gaggauta Yanke Hukunci Kan Shari’un Da Suke Da Alaƙa Da Ta’addanci
Gwamnatin Tarayya ta bukaci alkalai su gaggauta gudanar da shari’o’in ta’addanci, garkuwa da mutane, fataucin bil’adama da sauran manyan laifukan tashin hankali, domin bada gudunmuwa wajen yaki da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar. Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya yi wannan kiran a bikin bude shari’a ta Kotun Daukaka Kara ta 2025/2026 da aka gudanar a Abuja. Ya ce dole kotuna su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da hukunta masu aikata laifuka cikin gaggawa.
A wajen taron, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa gwamnati ta tanadi sabbin gidaje da za su inganta jin daɗin alkalai domin su gudanar da aikinsu ba tare da wata tangarda ta rashin matsuguni ba. Fagbemi ya jaddada cewa shari’o’in ta’addanci na buƙatar kulawa ta musamman da hanzari, domin hakan yana karfafa yaki da masu aikata laifukan da ke barazana ga rayuka da dukiyoyi. Ya ce gwamnatin Tarayya tana bin dabarun soja da na diflomasiyya tare da aiwatar da shari’a cikin sauri domin murkushe ta’addanci da sauran manyan laifuka.
A cewar Fagbemi, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kuduri aniyar ƙara yawan alkalan Babban Kotun Tarayya domin hanzarta gurfanar da wadanda ake zargi da laifukan ta’addanci da sauran shari’o’i da ke jinkiri a manyan kotuna. Kakaki24 na lura da cewa Ministan ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan shari’o’in da ke makale, tare da tabbatar da adalci cikin kankanin lokaci. Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su hada kai wajen yakar ta’addanci da duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya.
