Connect with us

Featured

A Gaggauta Janye Ƴansanda Daga Bawa Manyan Mutane Kariya – Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jan hankalin hukumomin tsaro da su gaggauta aiwatar da umarninsa na cire ’yan sanda daga rakiyar manyan mutane (VIPs). Ya yi hakan ne kafin zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan jinkirin aiwatar da tsarin da ya tsara domin ƙarfafa tsaron tituna da yankuna.

Tinubu ya umurci Ministan Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, IGP Kayode Egbetokun da NSCDC su tsara yadda za a maye gurbin jami’an da aka cire ba tare da an bar jama’a cikin haɗari ba. Ya ce dole ne a tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake buƙata, tare da ba da makamai ga Forest Guards domin hana sace-sacen mutane da barna a dazuzzuka. Ya kuma jaddada cewa VIPs da ke buƙatar kariya su koma amfani da Civil Defence kamar yadda umarninsa na 23 ga Nuwamba ya tanada.

Kakaki24 ta tattaro cewa shugaban kasar ya kuma mika babban aikin sake fasalin kiwon dabbobi ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, domin ta hannun NEC a tantance makiyaya da gonaki da za a mayar da su ranchuna. Ya ce hakan zai rage rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da ƙara ƙarfin tattalin arzikin kiwo a karkara.

A gefe guda kuma, maganganun Wole Soyinka sun sake janyo cece-kuce bayan da ya ce ya ga babbar tawagar tsaro na rakiyar Seyi Tinubu. Soyinka ya nuna mamaki kan yawan jami’an, yana mai cewa hakan na cin karo da matakin gwamnati na rage tsaro a hannun VIPs, lamarin da ya ƙara matsa lamba ga gwamnati wajen tabbatar da adalci a sabon tsarin tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet