Featured
Doka a Najeriya a Takarda Kawai Take Aiki – Osunbor

Mai ba da shawara kan doka na jam’iyyar ADC, Prof. Oserheimen Osunbor, ya bayyana cewa dokar ƙasa a Najeriya ta rage aiki ne a takarda kawai, inda ya zargi manyan sassan gwamnati uku da watsi da ƙa’idojin kundin tsarin mulki. Osunbor ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, a Legas, yayin wani taron nazari na yini guda da aka shirya domin bikin cika shekaru 90 na Cif Oladipo Jimilehin.
Tsohon gwamnan Jihar Edo ɗin ya ce a baya, har ma a zamanin mulkin soja, ana nuna wani mataki na mutunta doka, amma a yanzu a tsarin dimokuraɗiyya lamarin ya taɓarɓare. Ya soki Majalisar Tarayya, yana cewa ta rasa ‘yancinta ta koma “hatimin amincewa” ga bangaren zartarwa, inda take amincewa da buƙatun shugaban ƙasa ba tare da cikakken bincike ba, sabanin yadda take iya ƙin ministoci ko karya veto a baya.
Game da ɓangaren shari’a kuwa, Osunbor ya nuna damuwa kan jinkirin sauraron manyan shari’o’in siyasa da kuma zargin rashin aiwatar da wasu hukuncin Kotun Koli, yana mai cewa hakan ya rage amincewar jama’a da adalci. Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da raina kundin tsarin mulki daga bangarori uku na gwamnati na iya raunana dimokuraɗiyya tare da haifar da rashin kwanciyar hankali, inda ya buƙaci a ɗauki matakan gaggawa domin dawo da martabar dokar ƙasa a Najeriya.