Connect with us

Featured

John Cena Ya Yi Bankwana da Wasan Kokawa (WWE) Bayan Shafe Shekaru 24 Yana Jan-zarensa

Fitaccen jarumin damben WWE, John Cena, ya sanar da ritayarsa daga fagen damben ƙwararru a ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2025, bayan ya sha kaye a wasan bankwana da ya yi a Capital One Arena da ke Washington, D.C. Cena mai shekaru 48 ya mika wuya ne bayan Gunther ya kulle shi da “sleeper hold” a wasan da ya ɗauki kusan mintuna 25, abin da ya kawo ƙarshen daya daga cikin babban wasa mai cike da tarihi a WWE.

Masoya da dama sun nuna alhini da kuka yayin da Gunther ya ci gaba da rikon karshe duk da ihun magoya baya na roƙon Cena ya ci gaba. Bayan ya mika wuya — lamarin da ba kasafai yake faruwa ba a rayuwarsa ta dambe — ’yan wasa daga ɗakin sauya kaya na WWE suka shigo filin domin girmama shi. Daga nan Cena ya cire bandejin hannunsa da takalmansa ya bar su a cikin zobe, alamar bankwana ta gargajiya, kafin ya yi wa magoya baya gaisuwa ya fice.

John Cena ya yi ritaya a matsayin zakaran duniya sau 17, mafi yawa a tarihin WWE, tare da jagorantar WrestleMania sau shida. Ya fara harkarsa a 2002, ya yi fice da salon “Doctor of Thuganomics,” kuma ya yi suna da taken “You Can’t See Me.” Bayan dambe, Cena ya kuma yi nasara a harkar fina-finai. Ya sanar tun a Yulin 2024 cewa zai yi ritaya a ƙarshen 2025, inda yawon bankwanarsa ya haɗa da sauyin hali, lashe kambun duniya karo na 17, da kuma karshe shan kaye a SummerSlam.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet