Featured
Zage-zage Ba Zai Sa Na Daina Goyon Bayan Tinubu Ba – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba ya nadamar fito-na-fito da ya yi wajen goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu tun shekarar 2022, yana mai cewa suka da zage-zage daga wasu bangarori ba su taba girgiza matsayinsa ba. Wike ya bayyana haka ne yayin wani taro na musamman da aka shirya domin murnar cikar sa shekaru 58 da haihuwa a Abuja, inda ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya kasance kafin, lokacin da kuma bayan zaben shugaban kasa na 2023.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, ya fitar, Wike ya ce dukkan matakan siyasar da ya dauka sun samo asali ne daga ka’idojin gaskiya da mutunci. Ya tuno cewa shi ne kadai daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP da ya fito fili ya mara wa Tinubu baya a gaban jama’a, bisa hujjar adalci, daidaito da kuma bukatar mika mulki zuwa Kudancin kasar nan. Ya kuma ce nasarorin zabe a Jihar Rivers a lokacin da yake gwamna sun tabbatar da karfin jagorancinsa, inda APC ta lashe zaben shugaban kasa, yayin da PDP ta lashe sauran manyan zabuka a jihar.
Wike ya fara nuna goyon bayansa ga Tinubu ne bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP sakamakon fitowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2022, wanda ya ce ya sabawa tsarin karba-karba na jam’iyyar. A wajen bikin, manyan ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban sun yabawa Wike, suna bayyana shi a matsayin gogaggen dan siyasa mai tasiri a fadin kasa, tare da alkawarin ci gaba da mara masa baya, suna mai jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yi zabin da ya dace wajen daukar sa aiki daga PDP.