Connect with us

Featured

ICPC Za Ta Binciki Shugaban NMDPRA Kan Zargin Cin Hanci

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (ICPC) ta bayyana cewa za ta gudanar da cikakken bincike kan ƙorafin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shigar kan shugaban Hukumar Kula da Sarrafa da Sufurin Man Fetur a Najeriya (NMDPRA), Ahmed Farouk, bisa zargin cin hanci da almundahanar kuɗaɗen gwamnati. Dangote ya miƙa ƙorafin ne a ranar Talata, 16 ga Disamba, 2025, ta hannun lauyansa.

A cewar sanarwar da kakakin ICPC, John Odey, ya fitar, Dangote ya zargi Ahmed Farouk da kashe sama da dala miliyan bakwai wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu da ke ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, ba tare da bayyana sahihiyar hanyar samun kuɗin ba. Ƙorafin ya kuma nuna cewa ana zargin Farouk da amfani da muƙaminsa a NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin kansa, lamarin da ake cewa ya janyo asara ga ’yan Najeriya.

A nasa martanin, shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk, ya ce yana maraba da binciken da ICPC za ta gudanar, yana mai bayyana cewa binciken zai taimaka wajen fayyace gaskiyar lamarin da kuma wanke sunansa. Ya ƙara da cewa ba zai shiga musayar zarge-zarge a bainar jama’a ba, sai dai zai bari hukumomin da abin ya shafa su yi aikinsu yadda ya dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet