Connect with us

Featured

Ina Maraba Da Binciken ICPC a Kaina – Farouk Ahmed

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Najeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed, ya bayyana cewa ƙarar da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya kai shi gaban hukumomi wata dama ce gare shi ta wanke kansa daga dukkan zarge-zargen cin hanci da almundahana da ake yi masa.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, Ahmed ya ce yana maraba da duk wani bincike na hukuma, yana mai jaddada cewa irin wannan mataki zai ba da damar gudanar da bincike cikin adalci da tsantseni domin a fayyace gaskiya. Ya kuma ce ba zai shiga ce-ce-ku-ce da Dangote a bainar jama’a ba, yana mai nuna cewa bin doka da tsarin binciken hukuma shi ne hanya mafi dacewa.

Shugaban na NMDPRA ya ƙara da cewa hukumar da yake jagoranta tana aiwatar da ayyukanta bisa doka da ƙa’ida, tare da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin man fetur. Wannan dai na zuwa ne bayan da, a jiya Talata, Hukumar Yaƙi da Almundahana ta Ƙasa (ICPC) ta sanar da shirin fara bincike kan zargin da Aliko Dangote ya yi wa Farouk Ahmed.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet