Connect with us

Featured

Majalisa Ta Amince Mai Neman Takarar Shugabancin Ƙasa Ya Kashe Naira Biliyan 10 Yayin Yaƙin Neman Zaɓe

Majalisar Wakilai ta ƙasa ta amince da ƙarin iyakar kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe ga masu neman muƙaman siyasa, inda ta ɗaga na shugabancin ƙasa daga ₦5 biliyan zuwa ₦10 biliyan, sannan na gwamna daga ₦1 biliyan zuwa ₦3 biliyan. Wannan mataki ya zo ne a zaman majalisar da aka gudanar a Jumma’a, 19 ga Disamba, 2025, yayin nazari kan ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2025, bayan rahoton kwamitin Majalisar kan harkokin zaɓe.

Haka kuma, majalisar ta amince da wajabta wa INEC rika tura sakamakon zaɓe kai-tsaye ta lantarki zuwa IREV bayan an kammala sa hannu a takardun sakamako a rumfar zaɓe. An kuma ƙara iyakar kuɗin yaƙin neman zaɓe ga sanatoci zuwa ₦500 miliyan, ‘yan Majalisar Wakilai ₦250 miliyan, tare da saka iyaka ga gudummawar mutum ko kamfani zuwa ₦500 miliyan kacal ga kowane ɗan takara. Sai dai masana siyasa sun nuna damuwa cewa wannan tsari zai ƙara nesanta talakawa daga siyasa tare da ƙarfafa sayen ƙuri’a.

A cewar Kakaki24, majalisar ta kuma ƙara hukunci kan masu saye da sayar da ƙuri’a zuwa shekaru biyu a gidan yari ko tara ₦5 miliyan, tare da haramta musu tsayawa takara na tsawon shekaru 10. Duk da haka, ‘yan majalisar sun yi watsi da ƙudirin da ke neman hukunta rinjayar wakilai a zaɓen fidda gwani, suna masu cewa hakan na iya zama tarko a kansu, yayin da kungiyoyin farar hula suka yaba da amincewa da tura sakamako ta lantarki a matsayin hanyar dawo da amincewar jama’a ga zaɓe.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet