Featured
Harin Bam Ya Hallaka Masallata 5, Tare Da Jikkata 35 a Maiduguri

Aƙalla masallata biyar sun rasa rayukansu, yayin da mutane 35 suka jikkata sakamakon fashewar bam da aka kai Masallacin Juma’a na Gamboru da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin Alhamis, 24 ga Disamba, 2025, a lokacin da ake sallar Magariba, inda rahotanni suka nuna cewa mai harin kunar bakin wake ne ya tayar da bam a cikin masallacin.
Waɗanda suka tsira daga harin sun bayyana cewa wanda ake zargin ya shiga masallacin ne a farkon sallar, inda ya tayar da bam ɗin a raka’a ta farko, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da kuma Asibitin Kwararru na Jihar Borno, yayin da hukumomin tsaro da na agaji suka kai ɗauki cikin gaggawa.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno ta tabbatar da adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka jikkata, tare da cewa bincike ya fara domin gano cikakken bayani kan harin. Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira ga ƙara tsaurara tsaro a wuraren ibada, musamman a wannan lokaci na bukukuwa. Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.