Featured
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Jingine Fara Aiwatar da Sabuwar Dokar Haraji
Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta jingine fara aiwatar da sabuwar dokar haraji, sakamakon ce-ce-ku-ce da zargin an sauya wasu sassa bayan majalisa ta amince da su. Ɓangaren marasa rinjaye sun ce dole a dakata har sai an kammala bincike kan lamarin.
Buƙatar ta biyo bayan bambance-bambancen da aka gano tsakanin dokokin da majalisa ta amince da su da kuma waɗanda shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a kai, lamarin da ya haifar da ruɗani a tsakanin sassan gwamnati da al’ummar ƙasa.
Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta zargin, inda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce dokar za ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, yana mai cewa idan akwai matsala, daga ɓangaren majalisa take, yayin da majalisar ta kafa kwamitin bincike kan batun.
