Featured
NNPP Kano: Duk Masu Shirin Fita Daga NNPP Suyi Haƙuri Su Zauna – Dungurawa

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf da duk wanda zai bi shi zuwa APC sun yi hakan ne da raɗin kansu, yana mai jaddada cewa jam’iyyar NNPP ba ta amince da sauya sheƙar ba kuma ta yi iya ƙoƙarinta don hana faruwar hakan.
Dungurawa ya bayyana cewa jagorancin NNPP na Kano da na ƙasa, ƙarƙashin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun roƙi gwamnan da ya hakura saboda hakkin jam’iyya da jama’ar Kano, amma duk da haka abubuwa sun gagara. Ya ƙara da cewa abin da ke faruwa ba da amincewar su ba ne.
Sai dai ya sake roƙon gwamnan da duk masu shirin barin NNPP da su “mayar da wuƙarsu kube,” suna masu neman su ji tsoron Allah da Annabi, su zauna a jam’iyyar da talakawa da masu zaɓe suka amince da ita, maimakon komawa wadda aka yi hamayya da ita.
A ƙarshe, Dungurawa ya musanta jita-jitar cewa shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da mataimakin gwamna, Sanusi Surajo da Sanata Rufai Hanga, su ne suka haɗa gwamna Abba da Sanata Kwankwaso kan sauya sheƙa, yana mai cewa duk wanda ke da shaida ya fito da ita.