Featured
Muna Maraba da Shigowar Gwamnan Kano – APC

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take ta karɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf hannu biyu idan ya yanke shawarar barin NNPP ya koma APC, lamarin da ke ƙara ɗaga zazzafar muhawara a siyasar jihar.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya ce shigowar gwamnan zai ƙara ƙarfin jam’iyyar tare da ba ta damar samun rinjaye a zaɓen 2027, musamman ganin rahotannin da ke cewa ana sa ran gwamnan zai sauya sheƙa a farkon Janairu 2026.
Sai dai NNPP ta yi watsi da wannan shiri, tana kira ga Gwamna Yusuf da ya ci gaba da zama a jam’iyyar, inda masana siyasa ke cewa wannan yunkuri na iya sauya fasalin siyasa a Kano gabanin babban zaɓe.