Featured
Darren Fletcher Ya Zama Sabon Kocin Manchester United

Darren Fletcher, tsohon ɗan wasan tsakiyar Manchester United, ya maye gurbin Rúben Amorim a matsayin sabon mai horaswar ƙungiyar na riƙon ƙwarya, bayan da aka sallami mai horaswar ƙungiyar Ruben Amorim.
Hukumar gudanarwar Manchester United ta tabbatar da ɗaukar Fletcher nan take, domin kawo sabon salo da kwarin gwiwa ga ‘yan wasa a halin da ƙungiyar ke ciki. Wannan mataki ya biyo bayan rashin nasara da ƙungiyar ta fuskanta a wasannin baya-bayan nan.
Masu sharhi na ganin wannan sauyi na iya zama dama ga Manchester United don sake daidaita harkokinta, yayin da Fletcher ke shirin jagorantar tawagar har sai an kammala zabin kocin dindindin. Wannan sabon shugabanci na wucin gadi ya kawo sabon fata ga magoya bayan Red Devils.