Connect with us

Featured

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda a Borno da Kogi

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda biyar tare da ceto fararen hula uku da aka sace a yayin wani farmaki da suka kai a Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno. Aikin, wanda aka gudanar da safiyar Lahadi 04 ga Janairu, ya gudana ne tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force, inda aka fafata da ‘yan ta’addan a wani sanannen wurin ketarewa a yankin Sojiri.

Wata sanarwa daga Jami’in Yada Labarai na rundunar, Lt. Col. Uba Sani, ta bayyana cewa babu wani soja da ya jikkata yayin artabun. Ya ce an kwato bindigogi kirar AK-47 da wasu kayayyaki, tare da tabbatar da cewa nasarar ta nuna kwarewa da jajircewar sojoji wajen kare fararen hula da murkushe ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

A wani bangare kuma, sojin Nijeriya a Lokoja sun kashe ‘yan bindiga uku a wasu hare-hare daban-daban a Kabba Bunu da Yagba West na Jihar Kogi. An gudanar da ayyukan ne a ranar 3 ga Janairu, 2026, bisa sahihan bayanan sirri, inda aka kwato makamai, harsasai, tare da cafke wani da ake zargin mai samar wa ‘yan bindigar kayan abinci, yayin da gwamnatin jihar Kogi ta jaddada kudurinta na ci gaba da murkushe masu aikata laifuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet