Featured
Gwamnatin Gombe Ta Haramta Sana’ar Jari-Bola

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da haramta sana’ar jari bola a duk faɗin jihar, bisa dalilai da suka shafi tsaro. An yanke wannan shawara ne bayan taron Majalisar Tsaro ta Musamman da manyan jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, domin duba sabbin ƙalubalen tsaro a jihar.
Gwamnatin ta ce haramcin zai fara aiki nan take, kuma zai ci gaba har sai an tsara harkar sana’ar ƙarƙashin shugabanci da kulawa ta musamman. Ta bayyana cewa a baya-bayan nan ta samu rahotannin satar kayan more rayuwa da lalata kadarorin gwamnati da na makarantu, waɗanda ake zargin suna shiga hannun masu sana’ar jari bola.
Majalisar Tsaron jihar ta nuna damuwa kan yadda rashin tsari da shugabanci a cikin sana’ar ke kawo cikas ga sanya ido da kula da ayyukanta. Gwamnatin ta kuma ce nan gaba za ta kafa kwamitin aiwatarwa da sa ido, domin tabbatar da bin doka a dukkan ƙananan hukumomin jihar.