Featured
INEC Ta Cigaba Da Rijistar Zaɓe a Faɗin Najeriya

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake fara aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) a faɗin Nijeriya, wanda ke nuna fara zangon na biyu na shirin. Kakakin shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya tabbatar da cewa matakin ya fara aiki daga ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026.
INEC ta ce zangon farko na rijistar ya ƙare a ranar 10 ga Disambar 2025, inda sama da mutum miliyan 9.8 suka fara rijista ta yanar gizo. Daga cikin su, sama da mutum miliyan 2.5 ne suka kammala rijistar gaba ɗaya ta yanar gizo da kuma ta hanyar halartar cibiyoyi a faɗin ƙasar.
Hukumar ta ƙarfafa ’yan ƙasa da suka cancanta da su yi amfani da wannan dama domin yin rijista, sauya wurin kaɗa ƙuri’a ko sabunta bayanansu, sai dai ta ce aikin CVR bai shafi Jihar Anambra da Babban Birnin Tarayya Abuja ba a halin yanzu. INEC ta ce za ta sanar da sabon lokacin fara rijistar a waɗannan wurare nan gaba.