Featured
INEC Ta Gargadi Jama’a Kan Shafin Daukar Ma’aikata Na Bogi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta fitar da sanarwar gargadi ga al’ummar Najeriya kan wani shafin intanet na bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa shi ne shafin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi na shekarar 2026.
INEC ta bayyana cewa shafin ba shi da wata alaƙa da hukumar, inda ta jaddada cewa dukkan bayanai, ƙididdiga da takardun neman aiki da ke cikinsa ƙarya ne, kuma an ƙirƙire su ne da nufin yaudarar jama’a.
Hukumar ta ce tana gudanar da ɗaukar ma’aikata ne kawai ta shafinta na hukuma mai suna INECPRES, tare da shawarci jama’a da su guji bayar da bayanan sirri kamar BVN ko bayanan asusun banki, sannan duk wanda ya yi rajista a shafin bogi ya dakatar nan take.