Featured
Mun Kama Babban Dillalin Kwayoyin Da Ya Kashe Jami’anmu 3 a Shekarun Baya – NDLEA

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta cafke Lekan Jimoh, wanda aka fi sani da “Kanmo-Kanmo”, bayan shafe shekaru 12 ana nemansa bisa zargin kashe jami’an NDLEA uku a Jihar Ogun. An kama shi ne a ranar Juma’a, 16 ga Janairu, 2026, a garin Owode bayan sahihan bayanan sirri.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce Jimoh yana jerin wadanda ake nema tun 15 ga Yuni, 2014, lokacin da ake zargin ya jagoranci kai hari kan jami’an NDLEA da suka yi yunkurin kama shi. A yayin binciken maboyarsa, an kwato kilo 69 na skunk, wani nau’in tabar wiwi.
NDLEA ta ce kama Jimoh babban nasara ce wajen tabbatar da cewa babu wanda zai tsere wa hukunci ko da bayan dogon lokaci. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da kokarin jami’ai tare da jaddada kudirin NDLEA na ci gaba da farautar dillalan kwaya da karya hanyoyin safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.