Featured
Gwamnan Kano Zai Karɓi Katin Jamiyyar APC a Ranar Talata – Abdullahi Abbas

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai karɓi katin zama ɗan jam’iyyar APC ta hanyar na’ura (e-membership) a ranar Talata, 20 ga Janairu, 2026, kamar yadda jam’iyyar ta sanar.
Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ne ya bayyana hakan yayin wani taron jam’iyyar da aka gudanar domin shirya fara rijistar mambobi ta zamani da sabunta rajistar tsofaffin mambobi.
Abdullahi Abbas ya ce shirin rijistar ta na’ura wani mataki ne na ƙasa baki ɗaya da APC ke ɗauka domin tsaftace kundin mambobinta, da tabbatar da sahihancin bayanan dukkan ’yan jam’iyyar.
Ya kara da cewa wasu gwamnonin APC, ciki har da gwamnan Jihar Edo, tuni suka amfana da shirin, yayin da jihohi irin su Sokoto ke ci gaba da aiwatar da rijistar domin ƙarfafa jam’iyyar da tsarinta.