Featured
Gobara Ta Lalata Ajujuwa 34 a Makarantar Kiwon Lafiyar Dabbobi a Kano

Wata gobara da ta tashi a ranar Litinin ta cinye ajuzuwa 34 a wata Makarantar Kiwon Lafiyar Dabbobi da ke Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano. Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da misalin karfe 2:53 na rana.
A cewar sanarwar kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, cibiyar karɓar kiran gaggawa ta samu sanarwa daga wani Jamilu Abubakar, inda aka tura jami’ai daga tashar Rijiyar Zaki zuwa wajen.
Sanarwar ta bayyana cewa ajuzuwa 16 sun kone ƙurmus, yayin da 18 suka lalacewa, amma an shawo kan gobarar kafin ta bazu zuwa sauran gine-gine. Ba a samu asarar rai ba, kuma ba a bayyana musabbabin gobarar ba har zuwa lokacin hada rahoton.