Featured
Sojojin da Suka Yi Yunƙurin Juyin Mulki Sun Sanya Sunana Cikin Waɗanda Za a Kama Ko a Kashe – Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce an sanya sunansa daga cikin mutanen da masu yunkurin juyin mulki suka shirya kamawa ko harbewa idan ya ƙi biyayya. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi 01 ga Fabrairu 2026.
Musa ya ce ya taka rawar gani wajen taimaka wa hukumomin tsaro murƙushe shirin tun kafin ya yi ƙamari, yana mai bayyana masu yunkurin a matsayin mutane marasa tsari. Ya ce masu shirin ba su fahimci tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya da ƙarfin sojojin ƙasar ba.
Ministan ya ƙara da cewa mafi yawan waɗanda ke da hannu a lamarin an kama su, inda kaɗan ne kawai suka rage. Ya ce binciken ya nuna shirin ya samo asali ne daga ƙorafin wani jami’in soja da bai samu ƙarin girma ba, yana mai jaddada cewa aiwatar da juyin mulki a Najeriya a wannan zamani abu ne kusan ba zai yiwu ba.