Featured
DSS Na Shirin Gayyatar Wasu Mutane Kan Ɓacewar Dadiyata

Hukumar tsaron farin kaya ta (DSS) ta sake buɗe bincike kan bacewar Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata. An sace shi ne a ranar 2 ga Agusta, 2019 daga gidansa da ke Barnawa a Kaduna, kuma har yanzu ba a san inda yake ba. Sai dai a halin yanzu DSS na shirin gayyatar wasu mutane domin amsa tambayoyi kan lamarin.
Matarsa Kadijah ta bayyana damuwarta a wata hira da Reno Omokri, inda ta roƙi ‘yan Najeriya su taimaka wajen gano halin da mijinta ke ciki. Ta ce har yanzu suna fatan wata rana zai dawo gida. Reno Omokri ya kuma yi alƙawarin neman adalci tare da tallafa wa iyalansa.
Lamarin ya sake ɗaukar sabon salo bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya musanta hannu a ciki, yana mai cewa bai san Dadiyata ba kafin faruwar lamarin. Shi ma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ƙaryata alaƙanta shi da batun. Wata majiya ta tsaro ta ce DSS ta ƙwace fasfo ɗin El-Rufai tare da shirin gayyatar ‘ya’yansa domin amsa tambayoyi.