Featured
Arewacin Najeriya Na Cikin Jini, Amma Al’ummar Yankin Sun Fi Mayar da Hankali Kan Rikicin Iran/Isra’ila

Rayuwar al’ummar Arewacin Najeriya na ci gaba da salwanta cikin fargaba da rashin tabbas yayin da wasu jaridu, shahararrun mutane masu tasiri a kafafen sada zumunta, da matasa ke karkatar da hankali kan rikicin Iran da Isra’ila. Duk da yadda zubar da jini ke karuwa a jihohin yankin, al’ummar Arewa na ci gaba da watsi da halin da suke ciki, lamarin da ke kara nuna rashin kishi da kulawa da rayukansu.
Binciken Kakaki24 ya gano cewa, a watan Fabrairun shekarar 2026, hare‑hare da dama sun yi sanadiyar mutuwar mutane a jihohin Neja, Kwara, Kebbi da Adamawa. A Jihar Neja, a kauyen Kasuwan‑Daji, maharan sun kashe sama da mutane 30, sun yi garkuwa da wasu, sannan sun ƙona kasuwa da gidaje masu yawa, lamarin da ya tilastawa mutane da yawa guduwa don neman tsira.
Hukumar Niger State Emergency Management Agency (NSEMA) ta bayyana cewa fiye da mutane 30,000 sun bar gidajensu saboda fargabar hare-haren ƴanbindiga.
A Jihar Kwara, harin da aka kai a ƙauyen Woro ya yi sanadiyar kashe akalla mutane 170, yayin da wasu da dama aka yi garkuwa da su, aka kuma ƙona gidaje da kasuwanni da dama. A ƙarshen watan Fabrairu, harin ƙauyen Gada Oli ya sake jefa al’umma cikin tsoro da firgici,duk da ba’a samu asarar rai ba, amma an sace kayyaki da dama.
A Jihar Kebbi, ‘yan bindiga sun kai harin da ya shafi ƙauyuka da dama, ciki har da harin Dadinkowa, inda akalla mutane 5 suka mutu, wasu kuma suka ji rauni. A Jihar Adamawa, maharan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun hallaka fararen hula a Shuwari/Madagali, sun lalata dikiyoyi, sun jikkata wasu, yayin da mutane da yawa suka tsere daga gidajensu don neman tsaro.
A duk waɗannan jihohi, hare‑hare, sace‑sacen mutane da barazana ga rayuka na ci gaba da addabar al’umma. Duk da kokarin hukumomin tsaro na murƙushe kungiyoyin ta’addanci, halin da al’umma ke ciki na bukatar daukar matakan gaggauta.
Amma abin takaici, yayin da rayuka ke salwanta a gida, da yawan ‘yan Arewa masu tasiri a kafofin sada zumunta sun fi mayar da hankali ne ga abin da ke faruwa a Iran da Isra’ila. Maganganunsu kan rikicin Gabas ta Tsakiya sun yawaita, suna manta da garkuwa da mutane, kashe fararen hula, da barazanar da ke ci gaba da addabar yankinsu. Abinda ke sanya alamar tambaya kan cewa : shin akwai burin ganin an kawo karshen zubar da jini a Arewacin Najeriya ?.
Idan al’ummar Arewacin Najeriya da mutane masu amfani da kafofin sada zumunta zasu yawaita rubuce-rubuce da yin Allah-wadai tare da kira ga mahukunta kan gaggauta daukar matakin kan halin da yankin yake ciki kamar yadda suka yawaita maganganu da Allah-wadai kan rikicin Iran da Isra’ila tabbas za a samu sauki na wannan yanayi da ake ciki. Wannan rashin kulawa daga wasu daga cikin mutane Arewacin Najeriya yana kara jefa yankin cikin mummunan yanayi mai cike da damuwa, fushi da takaici.