Featured
Fiye da Mutane 1,300 Ne Suka Mutu a Iran Tun Bayan Fara Ƴaƙi da Isra’ila – Gwamnati

Gwamnatin Iran ta bayyana cewa mutane 1,332 ne suka mutu tun bayan fara yaƙin da ƙasar ke yi da United States da kuma Israel.
Rahotanni sun nuna cewa adadin ya haɗa da fararen hula da dama, ciki har da mata da yara, yayin da dubban mutane suka jikkata sakamakon hare-haren jiragen sama da rokoki da aka kai a sassa daban-daban na ƙasar.
Gwamnatin ta kuma ce hare-haren sun shafi wasu cibiyoyin kiwon lafiya, lamarin da ya ƙara taɓarɓarewar halin jin ƙai a wasu yankuna da rikicin ya shafa.