Featured
Mutum 31 Sun Mutu A Hare-haren da Isra’ila Ta Kai Beirut Da Kudancin Lebanon

Hare-haren sama da Israel ta kai kan birnin Beirut da kudancin Lebanon sun kashe mutum 31 tare da jikkata 149, a cewar ma’aikatar lafiyar ƙasar. Sanarwar ta ce adadin na wucin gadi ne yayin da ake ci gaba da tantancewa.
Babban hafsan rundunar sojin Isra’ila, Eyal Zamir, ya ce sojojin sun fara wani farmaki da ya kira “gagarumin shiri” kan ƙungiyar Hezbollah, wanda zai iya ɗaukar kwanaki da dama.
Tashin hankalin yankin ya ƙaru ne bayan rikicin da ya biyo bayan kashe jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, a hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai. Ƙasashen duniya na nuna fargabar yiwuwar rikicin ya rikide zuwa cikakken yaƙi a Gabas ta Tsakiya.