Featured
Ba Mu Yi Alƙawarin Gudanar da Sahihin Zaɓe Ɗari-bisa-ɗari Ba – INEC

ShugabanHukumarZaɓe ta Ƙasa, Joash Amupitan, ya ce hukumar na da ƙwarin gwiwar tura sakamakon zaɓe ta na’ura a zaɓen 2027. Sai dai ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da cewa komai zai tafi daidai ɗari bisa ɗari ba.
Amupitan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi yayin wani taron jin ra’ayin jama’a, inda ya buƙaci ‘yan Najeriya su rage tsammani mai yawa. Ya ce hukumar za ta yi iya ƙoƙarinta wajen gudanar da sahihin zaɓe, amma ba za a rasa yiwuwar samun ƙalubale ba.
Ya jaddada cewa zaɓe ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya, tare da nuna muhimmancin ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a da gaskiya a hukumomi. Shugaban na INEC ya ƙara da cewa babban ƙalubalen shi ne batun aikawa da sakamakon kai tsaye a lokaci guda.