Featured
Rundunar Ƴansanda Ta Tabbatar da Fashewar Bama-bamai Uku a Maiduguri

Rundunar ‘yan sandan Borno ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan kunar bakin wake ne sun kai hare-haren abubuwan fashewa a wurare uku a Maiduguri da yammacin Litinin.
Mai magana da yawun rundunar, Nahum Daso, ya ce wuraren da abin ya shafa sun haɗa da University of Maiduguri Teaching Hospital, kasuwar Monday Market da kuma gadar Post Office , inda jami’an sashen lalubo bama-bamai ke ci gaba da aikin bincike da tsabtace wuraren.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu yayin da wasu da yawa suka jikkata sakamakon fashewar, lamarin da ya sa gwamnan jihar Babagana Zulum ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa abin takaici ne da aka kai hari ga fararen hula musamman a cikin watan Ramadan.