Addini
Saudiyya Ta Bayar da Umarnin Fara Duba Jinjirin Watan Sallah

Kotun Kolin Saudiyya ta yi kira ga mazauna ƙasar da su fara duban jaririn watan Shawwal a yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan na shekarar Hijira ta 1447 AH, wanda ya zo daidai da 18 ga watan Maris, 2026.
A cikin wata sanarwa da kotun ta fitar ranar Litinin, ta bukaci duk wanda ya ga jaririn watan da idanunsa ko kuma ta hanyar amfani da tabarau na musamman wajen hangen wata, ya gaggauta kai rahoto ga kotun da ke kusa da shi domin tabbatar da sahihancin ganin.
Kotun ta jaddada cewa sakamakon rahotannin da za a samu daga ganin watan ne zai ba da damar ayyana ranar da za a gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a faɗin ƙasar Saudiyya.
Rahoton ganin watan na da muhimmanci a tsarin tabbatar da ƙarshen watan Ramadan da kuma fara watan Shawwal, wanda ke alamta zuwan ranar Eid al-Fitr ga al’ummar Musulmi a sassa daban-daban na duniya.