Featured
INEC Ta Janye Ƙudirin Tabbatar da Sahihancin Rajistar Masu Zaɓe
Hukumar zaɓe ta ƙasa Independent National Electoral Commission (INEC) ta umarci kwamishinonin zaɓe na jihohi su dakatar da duk wani shiri da ya shafi sake tantance rajistar masu zaɓe. Wannan mataki ya biyo bayan damuwar da masana da jam’iyyun adawa suka nuna game da shirin.
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki shirin, tana mai cewa zai iya hana miliyoyin ‘yan Najeriya damar kaɗa ƙuri’a, musamman ganin yadda lokacin zabe ya karato. Haka kuma wani ɓangare na Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana lokacin aiwatar da shirin a matsayin abin da ke da ruɗani, yana zargin cewa hakan na iya zama yunƙurin takura wa masu zaɓe.
Wasu ƙungiyoyi da masana harkokin siyasa sun yi gargadin cewa duk wani tsari ya kamata ya tabbatar da kowa ya samu damar shiga zaɓe. Sai dai INEC ta ce manufar shirin ita ce tsaftace rajistar masu zaɓe da ƙarfafa sahihancin zaɓe, ba wai hana mutane damar yin zaɓe ba.
