Featured
JAMB Ta Nemi Afuwa Kan Jinkirin Sakin Sakamakon UTME

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Najeriya (JAMB) ta nemi afuwa kan jinkirin sakin sakamakon jarabawar UTME da aka gudanar ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026. Tun da farko hukumar ta sanar cewa za ta fitar da sakamakon a ranar Asabar, amma hakan bai samu ba, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin dalibai.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar, ya danganta jinkirin da rashin halartar shugaban hukumar saboda wani muhimmin aiki na hukuma. Ya tabbatar da cewa za a fitar da sakamakon a ranar Lahadi kafin dare, tare da ba daliban hakuri kan jiran da suka yi.
Tun da farko dai JAMB ta saki sakamakon rukunin farko na daliban da suka rubuta jarabawar ranar Alhamis, inda aka fitar da sakamakon dalibai 632,788. Haka kuma an shawarci dalibai su duba sakamakonsu ta hanyar tura sakon “UTMERESULT” zuwa lambobin 55019 ko 66019 da layin da suka yi rajista da shi.