Featured
JAMB Ta Saki Sakamakon UTME na Ranar Alhamis

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Najeriya (JAMB) ta sanar da sakin sakamakon daliban da suka rubuta jarabawar UTME ta 2026 a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu. Jimillar sakamako 632,788 ne aka ce sun fito.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar, an bukaci dalibai su duba sakamakonsu ta hanyar aika sakon “UTMERESULT” zuwa 55019 ko 66019 da layin wayar da suka yi rajista da shi. Sai dai an bayyana cewa a halin yanzu dubawa kawai ake iya yi, ba a fara bayar da damar bugawa ba.
Hukumar ta kuma gargadi dalibai da iyaye da su guji canza sakamakon da aka aiko ta SMS, tana mai cewa hakan laifi ne mai tsanani. Ta ce an riga an kama wasu mutane uku, ciki har da dalibai biyu da wani mahaifi, bisa zargin magudin sakamako ta hanyar amfani da fasahar zamani, tare da jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.