Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Horas da Tubabbun Ƴan Ta’adda Su 744

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mutane 744 da suka tuba daga ayyukan ta’addanci sun kammala karbar horo, inda suka gyara halayensu suke jiran sake shiga cikin al’umma. An gudanar da bikin kammala shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor.
Rahotanni sun nuna cewa yawancin wadanda suka kammala shirin daga jihar Borno ne, yayin da wasu kuma suka fito daga jihohin Najeriya daban-daban har ma da ƙasashen waje kamar Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar. An bayyana cewa an horar da su kan sana’o’i, ilimin rayuwa da kuma gyaran tunani.
Hukumomi sun ce shirin ba gafara ba ne, sai dai hanya ce ta rage tsattsauran ra’ayi da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa. An kuma yi kira ga jihohi da al’umma da su karɓe su tare da ba su goyon baya domin su zama ‘yan kasa masu amfani.