Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar da Wadanda Ake Zargi da Yunƙurin Juyin Mulki a Kotu
Gwamnatin Tarayya ta shigar da kara kan wasu da ake zargi da kitsa juyin mulki domin hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki. Ofishin Babban Lauyan Tarayya ne ya shigar da karar, karkashin jagorancin daraktan shari’o’in gwamnati, Rotimi Oyedepo.
Wadanda ake zargin sun hada da tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na Rundunar Ruwa, jami’in ɗan sanda mai mukamin Inspekta da wasu uku, inda ake tuhumarsu da laifukan cin amanar kasa, ta’addanci da kuma shirya yaki da Najeriya. Haka kuma, ana zargin wasu daga cikinsu da rike kudade masu alaka da daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Rahotanni sun ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ranar 22 ga Afrilu, yayin da takardun karar suka nuna cewa sun hada kai domin tayar da rikici da kuma boye bayanan tsaro da suka shafi shirin juyin mulkin.
