Featured
Kotu Ta Ɗage Sauraron shari’ar Buƙatar Bayar da Belin El-Rufai Zuwa Watan Yuni

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta dage sauraron hukunci kan bukatar beli da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya gabatar, inda ta mayar da shi zuwa makon farko na watan Yunin 2026.
Mai shari’a Darius Khobo ne ya yanke wannan hukunci bayan ci gaba da shari’ar da ake tuhumar tsohon gwamnan da laifukan da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukami ba daidai ba, wanda Hukumar ICPC ta shigar.
Lauyan El-Rufai ya soki yawan dage sauraron karar, yana mai cewa hakan na da nasaba da siyasa, yayin da tsohon gwamnan ya bayyana cewa akwai wani shiri na sake daure shi da kuma hana shi samun beli, inda aka tsaurara matakan tsaro a kotu yayin zaman shari’ar.