Featured
Tinubu Ya Amince da Kashe Naira Biliyan 15 Don Gina Makarantar Horas da Ƴansanda a Ogun

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabon reshen Kwalejin ‘Yan Sanda a Erinja da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun, tare da ware Naira biliyan 15 a matsayin kudin fara aiki.
Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce za a dauko kudin ne daga asusun TetFund na shekarar 2026 domin gina muhimman gine-gine, dakunan karatu, masaukin dalibai da kayan horo.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin karfafa tsaro a kasar, inda shugaban kasar ya jaddada cewa fadada makarantar zai inganta horo da shugabanci a rundunar ‘yan sanda, musamman bayan umarnin daukar karin jami’ai 20,000 domin tinkarar matsalolin tsaro.