Featured
Ficewar Obi Da Kwankwaso Za Ta Ƙara Mana Ƙaimi – David Mark

Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark, ya ce ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar za ta kara wa jam’iyyar kwarin gwiwar yin aiki tukuru. Ya kuma tabbatar da cewa ADC za ta fitar da ‘yan takara nagari wadanda za su lashe zaben 2027.
David Mark ya bayyana hakan ne ranar Laraba 06 ga Mayu, 2026 a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja yayin ganawarsa da tsofaffi da masu ci gaba da zama ‘yan majalisar dokoki a karkashin ADC. Ya ce duk da tasirin da ficewar manyan jiga-jigan biyu za ta yi, hakan zai sa jam’iyyar kara hada kai domin samun nasara a zabe.
A nasa bangaren, kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar ba ta damu da ficewar wasu ‘yan majalisa ba. Ya zargi wadanda suka fice da bin wasu jagorori ne saboda suna ganin za su taimaka musu wajen cin zabe, yana mai cewa har yanzu ginshiƙin jam’iyyar na nan daram.