Connect with us

Addini

Eid-ul-Adha: Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da Hutun Kwanaki Biyu Domin Bukukuwan Sallah

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Laraba 27 da Alhamis 28 ga watan Mayun 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid-el-Kabir. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta dauki matakin ne domin nuna girmamawa ga addinin Musulunci da kuma muhimmancin bikin Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya. Ministan ya taya Musulmai murnar bikin, yana mai bayyana Eid-ul-Adha a matsayin lokaci na sadaukarwa, biyayya ga Allah da kuma tausayi ga jama’a.

Tunji-Ojo ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin hutun wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, tsaro da ci gaban kasa. Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da kyakkyawar mu’amala yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet