Featured
INEC Ta Soke Duk Zaɓen Fidda-gwanin Da Aka Gudanar Bayan 30 Ga Mayu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa cewa duk wani zaben fidda gwani da aka gudanar bayan wa’adin ranar 30 ga Mayu, 2026 ba zai yi aiki ba, sai dai idan Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan lamarin.
Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Mohammed Kudu Haruna, ya ce jam’iyyu su ci gaba da bin tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 har sai an kammala sauraron karar da hukumar ta daukaka. Ya jaddada cewa duk wani zaben fidda gwani da ya sabawa jadawalin INEC na iya fuskantar matsala ta shari’a.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin INEC da wasu jam’iyyun siyasa kan jadawalin zabukan fidda gwani gabanin zaben 2027. Kakaki24 ta rawaito cewa INEC ta daukaka kara kan hukuncin kotu, yayin da wasu kotuna suka sake tabbatar da ikon hukumar wajen tsara jadawalin zabe muddin tana aiki cikin iyakar dokar zabe.