Featured
NDC Ta Amince da Mustapha Kwankwaso a Matsayin Mataimakin Gwarzo a Takarar Gwamnan kano a 2027

Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa Comrade Gwarzo ya zaɓi Mustapha Kwankwaso a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamnan jihar Kano gabanin zaɓen da ke tafe.
Sanarwar na kunshe ne a cikin bayanin da Kakakin Tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Habib Sale Mailemo, ya fitar, inda ya tabbatar da zaɓen Mustapha Kwankwaso domin mara wa Comrade Gwarzo baya a takarar.
Jam’iyyar ta ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryenta na tunkarar zaɓe, yayin da sanarwar ta jawo hankalin masu bibiyar harkokin siyasar Kano.