Featured
Ba za mu janye wa Atiku Abubakar ba – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba za su janye takararsu a zaɓen 2027 domin goyon bayan ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar ba.
Kwankwaso, wanda ke takara tare da Peter Obi, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da yaɗa jita-jitar cewa za su janye daga takarar.
Read Also : Kano za ta jagoranci Arewacin Najeriya wajen ganin an sake zaɓar Tinubu a 2027 — Abba Kabir Yusuf
Ya ce babu wani dalili da zai sa shi da Obi su janye daga zaɓen shugaban ƙasa domin goyon bayan Atiku ko wani ɗan takara. Ya kuma zargi ADC da mayar da hankali wajen sukar NDC maimakon gabatar da ƙwarewa da cancantar ɗan takararta.
Kwankwaso ya buƙaci ADC ta mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Kashim Shettima ya yi wa ɗan takararta, maimakon kai hari kan sa shi da Obi. Ya kuma ce tikitin NDC shi ne zaɓi mai inganci wajen magance matsalolin tsaro, ilimi, noma, lafiya da tattalin arziki.
Pingback: Gov. Buni Meets Chief Imams... Calls for More Prayers for Nigeria - KAKAKI 24