Featured
Kano za ta jagoranci Arewacin Najeriya wajen ganin an sake zaɓar Tinubu a 2027 — Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin tattara miliyoyin ƙuri’u domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana cewa Kano za ta kasance kan gaba tsakanin jihohin Arewa wajen nuna goyon baya ga jam’iyyar APC da Tinubu a zaɓen mai zuwa.
Read Also : Zaɓen 2027: Arewa za ta bai wa Tinubu ƙuri’u fiye da na 2023 — Shettima
Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wadda ke neman goyon bayan Tinubu.
Ya ce Kano, wadda ya bayyana a matsayin jiha mafi yawan masu ƙuri’a a Arewa, za ta tattara gagarumin goyon baya domin sake zaɓen Shugaban ƙasar a shekarar 2027.
Pingback: Ba za mu janye wa Atiku Abubakar ba - Kwankwaso - KAKAKI 24