Fashion
UAE Ta Haramtawa Yara Ƴan Ƙasa da Shekaru 15 Amfani da Shafukan Sada Zumunta

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da haramta amfani da kafafen sada zumunta ga yara ƴan ƙasa da shekara 15. Sabuwar dokar ta bai wa kamfanonin sada zumunta wa’adin watanni 12 su rufe asusun yaran da suka gaza kai wannan shekaru.
Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar kwakwalwa da tsaron yara daga cin zarafi ta intanet, masu yaudarar yara da kuma matsalar shaye-shayen ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta. Yara masu shekara 15 zuwa 16 za su iya amfani da manhajojin ne ƙarƙashin tsauraran ƙa’idoji.
Hukumomi sun gargaɗi cewa duk wata manhaja da ta gaza bin dokar, to za ta iya fuskantar takunkumi ko rufewa gaba ɗaya. Kakaki24 ta ruwaito cewa UAE ta zama ƙasa ta farko a yankin Larabawa da ta kafa irin wannan doka kan amfani da kafafen sada zumunta ga yara.