Connect with us

Addini

Fusatattun Matasa Sun Kone Malamar Islamiyya Har Lahira a Kaduna

Wasu fusatattun matasa sun kashe wata matar aure tare da kona ta da ranta a garin Maraban Jos da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, bayan zargin ta da satar yara. Lamarin dai ya haddasa tashin hankali tsakanin mazauna garin.

Rahotanni sun ce matar wadda malamar islamiyya ce, tana kan hanyarta ta zuwa wani taron wa’azin addini, inda ta tsaya tambayar wasu yara domin nuna mata hanya, amma sai aka yi rashin sa’a wasu mata suka zarge ta da yunkurin satar yara. Bayan jami’an tsaro sun ceto ta tare da kai ta ofishin ’yan sanda domin ba ta kariya da gudanar da bincike, daruruwan matasa sun mamaye ofishin suna neman a mika musu ita.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai wa matar harin ne bisa zarge-zargen karya wanda ba shi da tushe. Ya ce matasan sun kwace ta daga hannun ’yan sanda, inda suka kashe ta sannan suka kona gawarta. Rundunar ta ce ta kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da bincike da neman sauran wadanda ake zargi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet